Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Bayt (AS) - ABNA - Iran ta Musulunci ta cika da haske, farin ciki da jin dadin a ranar haihuwar Sayyidah Fatima Zahra (SA) mai albarka a yau. A wannan lokaci, an gudanar da wani biki mai cike da farin ciki na tunawa da wannan rana bisa halartar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da dubban masoyan Ahlul-Bait (AS)’ tare da rere wakokin farinciki girmamawa ga Sayyidah Fadimah As shugabar duniyoyi guda biyu.
A wannan biki, wanda ya dauki kimanin awanni uku, Jagora Ayatullah Khamenei ya taya murnar haihuwar Sayyidah Siddiqah Tahirah (AS), sannan ya ce: Al'ummar Iran, tare da juriyarsu ta kasa, sun dakile kokarin da makiya ke yi na canza "tushen addini, tarihi, da al'adu" na wannan al'umma, a yau kuma yayin da ya zama dole a shirya yadda ya kamata don bayar da kariya da kai hari kan farfagandar makiya da ayyukan kafofin watsa labaransa wacce take kai hari kan "hankula da kwakwale, zukata, da imani", Iran madaukakiya ta na ci gaba akan tafarkinta duk da matsaloli da tawayoyi da ke akwai a duk fadin kasar.
Yayin da yake taya murnar zagayowar haihuwar Imam Khumeini (RA) wanda ya dace da lokacin haihuwar sayyidah Fatima Zahra (SA), Jagoran juyin juya halin Musulunci ya siffanta falaloli da kyawawan halaye shugabar Duniyoyi Biyu da cewa sun wuce riska da fahimtar ɗan adam, sannan ya ƙara da cewa: Duk da wannan duka, dole ne mutum ya zama BaFatimiyye kuma ya yi koyi da wannan shugabar a dukkan fannonin rayuwarsa, ciki har da taƙawa, neman adalci, Jihadin bayyana gaskiya, yanayin zaman aure, renon yara, da sauran fannoni.
Ya ɗauki waken yabo a matsayin wani abu mai tasiri sosai, sannan ya ƙara da cewa: Ya zama dole a gudanar da bincike da nazari don zurfafawa acikinsa da gano wuraren kura-kurai, da kuma neman hanyoyin ƙarfafawa da haɓaka fannoni daban-daban na wannan lamari mai ban mamaki.
Da yake magana game da ci gaban waken yabo idan aka kwatanta da na baya, Ayatullah Khamenei ya kira waken yabo a matsayin ɗaya daga cikin tushen adabin gwagwarmaya, kuma ya ƙara da cewa: Duk wani tunani da abu zai kwaranye sannu a hankali idan har ya zamo babu adabi da ya dogara da shi mai dacewa, fannin wakokin yabo da majalisosin da ake gudanarwa, a yau, ta hanyar tattara adabin gwagwarmaya da faɗaɗa shi da yada shi suna ƙarfafa wannan muhimmiyar buƙata.
Jagoran juyin juya halin ya bayyana Jagoran juyin juya hali ya bayyana "gwagwarmayar kasa" a matsayin "juriya da gwagwarmaya ne ga dukkan nau'ikan matsin lamba daga azzalumai" kuma ya kara da cewa: Wani lokaci matsin lamba na soji ne; - kamar abin da al'umma ta gani da idonta a yakin kariya mai tsarki da abin da matasa da samari suka gani a cikin watannin da suka gabata - wani lokacin kuma matsin lamba ne na tattalin arziki ko na kafofin watsa labarai, al'adu da siyasa.
Jagoran juyin juya halin ya kira girman kan kafofin watsa labarai na Yamma da jami'an siyasa da sojoji alama ce ta matsin lambar farfagandar makiya kuma ya ce: Manufar matsin lamba daban-daban na tsarin shine mamaye ƙasashe,gaba gaba gare su sune al'ummar Iran ce; wani lokacin faɗaɗa yankuna ne; kamar abin da gwamnatin Amurka ke yi a Latin Amurka a yau.
Ya ƙara da cewa: "Wani lokaci manufar ita ce mamaye albarkatun ƙasa, wani lokacin kuma canza salon rayuwa, kuma mafi mahimmanci, "canza tushe da asali" shine babban burin matsin lambar azzalumai".
Da yake magana game da fiye da shekaru ɗari na ƙoƙarin da masu zaluntar duniya ke yi na canza asalin "addini, tarihi, da al'adu" na ƙasar Iran, Ayatullah Khamenei ya ce: Juyin juya halin Musulunci ya sa duk waɗannan ƙoƙarin sun zamo marasa amfani, kuma a cikin 'yan shekarun nan, al'ummar Iran ta wargaza su da juriyarta da tabbatuwarta duk da ci gaba da matsin lamba daga maƙiyanta.
Ya kira yaɗuwar ra'ayi da adabin gwagwarmaya da wata hakika data fito daga Iran zuwa ƙasashen yankin da wasu ƙasashe, yana mai ƙara da cewa: Wasu daga cikin ayyukan da maƙiya suka yi wa Iran da al'ummar Iran da ace za su aikata shi ga wa wata ƙasa da ya zamanto sun shafe su wannan ƙasar.
Your Comment